News
Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya makin samun gurbin karatu a bana
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya maki 140 zuwa sama a matsayin makin samun gurbin karatu na shekarar 2022/23 a jami’o’in kasar nan.
Rijistaran hukumar Farfesa Is-haq Oloyede ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron shekarar 2023 kan shiga manyan makarantu da bayar da kyaututtuka da aka yi ranar Asabar din nan a Abuja.
Oloyede ya ce an amince da 100 a matsayin makin samun gurbin karatu a kwalejojin fasaha Polytechnics da Kwalejojin Ilimi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Oloyede ya bayyana cewa abubuwan da aka ambata sune mafi ƙanƙanta, amma hakan ba yana nufin dole ne hukumomi su bi shi ba.
Advertisements
