News
Mutum Miliyan 165 Sun Faɗa Ƙangin Talauci Cikin Shekara Uku – MMD
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu ƙaruwar talauci a matalautan kasashe, inda adadin mutanen da ke rayuwa ƙasa da dala 3.65 a shekarar 2023 ya kai miliyan 165.
Cikin wani rahoton da Hukumar Raya Ƙasashe Ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta fitar ranar Alhamis, ya ce annobar Korona da hauhawar farashi da kuma yaƘin Ukraine sun tilasta wa mutum miliyan 165 shiga Ƙangin talauci tun shekarar 2020 zuwa 2023.
Dattijo Alhaji Tanko Yakasai Ya Bai Wa Gwamnatin Abba Shawarwari
Rahoton ya ambato shugaban Hukumar UNDP Achim Steiner ya ce ”Kasashen da suka zuba jari cikin shekaru uku da suka gabata, domin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi, sun taimaka wajen kare al’ummarsu da dama daga faɗawa ƙangin na talauci.
A yayin da ya ce ƙasashen da ba su yi wani hoɓɓasa wajen rage talaucin suka fi fuskantar matalar ƙaruwar matalauta a cikin al’ummominsu.
Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma yi kiran a sassauta wa ƙasashe masu tasowa biyan bashi.
”A yau ƙasashe 46 na kashe fiye da kashi 10 na kuɗin shigar da suke samu wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasashen”, in ji shi.
A cewar rahoton biyan bashi da ƙasashen ke yi na ƙara musu wahalhalu wajen tallafa wa talakawan cikinsu a bangarorin lafiya da ilimi da sauran bukatun rayuwa.
-
News2 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News10 hours ago
Jami’an Ƴansanda 98 Ne Suka Mutu A cikin Watanni 10 A Sassan Najeriya — Rahoto

