News
Gwamnatin Jihar Adamawa ta sanar da sassauta dokar hana fitar da ta sanya ta sa’o’i 24
DAGA VKABIRU BASIRU FULATAN.
Gwamnatin Jihar Adamawa ta sanar da sassauta dokar hana fitar da ta sanya ta sa’o’i 24 a Kananan Hukumominta 21, bayan wasoson kayan abincin da aka yi a rumbunan gwamnati da ke Jihar.
A ranar Lahadi ce dai rahotanni suka bayyana yadda wasu bata-gari suka rika farfasa rumbunan gwamnati a Yola, babban birnin jihar, inda suka rika dibar kayan abinci da na masarufi suna guduwa da su.
Amma a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Gwamna Ahmadu Fintiri, Humwashi Wonosikou, ya fitar ranar Litinin, ya ce a yanzu dokar ta koma daga 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Sanarwar ta ce sassauta dokar ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin shugabannin tsaro na jihar da jami’an gwamnati, wacce Mataimakin Gwamnan Jihar, Farfesa Kaletapwa George Farauta, ya jagoranta cikin dare.
Sanarwar ta kuma ce bayan sassauta dokar, jami’an tsaro za su ci gaba da sintiri don tabbatar da cewa an bi umarnin na gwamnati sannan bata-garin ba su sake kawo wa zaman lafiyar jihar tarnaki ba.
Daga nan sai gwamnatin ta shawarci iyaye da su kai ’ya’yansu makaranta da safe sannan wuraren kasuwancinsu ba tare da fargaba sannan su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai.
Mataimakin Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ba za ta zauna ta zuba ido bata-gari su ci gaba da kassara jihar ba.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
