Connect with us

News

APC DA NNPP: Manyan jam’iyyun siyasar Kano biyu sun koma ga Allah

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Manyan jam’iyyun siyasar Kano biyu sun koma ga Allah, a daidai lokacin da suke jiran hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar za ta yanke nan gaba.

Hukuncin kotun dai yana da matuƙar muhimmanci ga jam’iyyun NNPP mai mulki a ƙarƙashin jagorancin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma APC ta hamayya wadda Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke jagoranta.

Advertisement

Abinda Da Zai Kawo Karshen Juyin Mulkin Sojoji A Nahiyar Afirika–Shehu Sani

Magoya bayan jam’iyyar APC na ci gaba da tarukan addu’o’i da saukar Alƙur’ani a mazaɓu da ƙananan hukumomi, bayan azumin nafila da, da yawa daga cikinsu suka yi a ranar Litinin.

Ƴan jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano ne suka fara gudanar da salloli da kuma addu’o’in neman nasara a filin wasa na Ƙofar Na’isa sanye da jajayen huluna a ranar Asabar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending