Connect with us

News

UNICEF Za Ta Samar da Ginin Ma’aunin Harhada Adana a Jihar Kano

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

A kokarinta na tallafa wa gwamnatin jihar Kano wajen bunkasa harkokin kiwon lafiya, ma’aikatar lafiya ta tarayya ta hannun Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta shirya gina ma’aunin harhada magunguna a Kano.

Advertisement

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwar da Jami’in yada labarai na Ma’aikatar Lafiya ta Jahar Kano Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.

kotun karbar korafekorafen Zabe ta tabbatar da nasarar zaɓen Abdulmumin Kofa a matsayin ɗan majalisar dokoki a Kano

Da yake jawabi yayin mika wurin ga ‘yan kwangilar da su yi aikin daga UNICEF a harabar Hukumar Samar da Magunguna ta jihar Kano (DMCSA), a jiya, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce wannan babbar nassara ce da aka samu a fannin kiwon Lafiya a jahar Kano.

Advertisement

Ya bayyana cewa tuni UNICEF ta aiko da tawagarsu jihar domin fara aikin, inda ya ce wurin da za a gudanar da aikin yana cikin shalkwatar DMCSA da ke Kano.

Dakta Labaran ya ci gaba da cewa, inganta tsarin kiwon lafiya a jihar yana cikin tsarin da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi tun lokacin da ya tsaya takarar gwamnan jihar Kano.

Advertisement

Ya jaddada cewa inganta samar da magunguna ga dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya na jama’a masu inganci kuma isassu da kuma rahusa ga dimbin al’ummar jihar wani tsari ne da aka tsara domin cimma burin mai girma Gwamna a fannin kiwon lafiya.

Kwamishinan ya yaba wa UNICEF bisa kawo wannan aikin jihar, yana mai ba su tabbacin hadin kan gwamnati da ci gaba da aiki da su da nufin samun ingantaccen tsarin kiwon lafiya domin ci gaban al’ummar jihar.

Advertisement

Shi ma da yake jawabi, Darakta Janar na DMCSA, Pharm. Gali Sule, ya bayyana cewa wannan wata manufa ce ta ma’aikatar lafiya ta tarayya da ke son kowace jiha ta samu akalla ma’aunin harhada magunguna guda daya.

Babban Darakta ya kuma bayyana cewa, aiki ne na hadin gwiwa, inda jihar Kano ke hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu da ke akin inganta tsarin kiwon lafiya ta hanyar ma’aikatar lafiya ta tarayya.

Advertisement

Pharm Gali, wanda ya nuna jin dadinsa da aikin, ya yi imanin cewa, aikin zai taimaka wa Hukumar wajen cimma burinta na lalubo tare da samar da ingantattun magunguna da suke isassu, masu nagarta da kuma rahusa ga dukkan cibiyoyin kula da lafiyar jama’a na jihar Kano.

A nata bangaren, Ko’odinetan ayyuka ta UNICEF, Lourdes Eleana, ta ce sun zu Kano ne domin samar da irin wannan ginin.

Advertisement

Ta bayyana cewa UNICEF za ta samar da irin wadannan gine-gine guda 22 a jihohi 21 na Najeriya kuma Kano na daya daga cikinsu, sannan ta ce sun ne da karbar wuraren da za a yi ginin, tana mai ba da tabbacin kammala aikin gaba daya a cikin watan Disamba na shekarar 2023.

A cewar Eleana, saboda yawan al’ummar jihar Kano, aikin zai amfanar da jama’arta sosai saboda ma’ajiyar sinadarai na kantin magani zai sa magungunan su kasance cikin yanayi mai kyau da kuma aminci da amfani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending