Connect with us

News

Mutane 4 sun mutu yayin da wata babbar mota dauke da kwantena ta murkushe Motoci uku 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Mutane hudu ne suka rasa rayukansu tare da jikkata wasu da dama, sakamakon wani hatsarin mota da ya afku a kan gadar Aba Waterside a Ogbor-Hill, a jihar Abia.

Vanguard ta ruwaito cewa hatsarin ya afku ne a yayin da wata babbar mota da ke dauke da kwantena mai tsawon kafa 40, ta rasa birki, ta kutsa cikin wata mota da babur mai kafa uku, inda ta kashe mutane hudu a nan take.

Advertisement

Kotu Ta Daure Mazambatan Yanar Gizo Biyu A Jihar Kano

Wani ganau ya shaida wa Jaridar Vanguard cewa motar a lokacin da take saukowa daga mahadar Opobo dake kan titin Aba Ikot zuwa Ekpene, ta karkace ne sakamakon fadowar da motar ta yi a kan gadar.

A lokacin da jaridar Vanguard ta ziyarci wurin, an ga mutanen hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC suna jagorantar zirga-zirgar ababen hawa.

Advertisement

Masu jajantawa sun yi kokarin ceto wadanda suka jikkata da wadanda suka makale a karkashin kwantena. Daya daga cikin fasinjojin da aka ceto a cikin babur din ta samu rauni a kafafunta, yayin da dayar ta samu munanan raunuka.

Wasu daga cikin masu jajantawa da lamarin ya faru, sun bayyana fushinsu ga jami’an hukumar FRSC kan jinkirin da aka samu wajen daukar motar daukar kaya domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda har yanzu suke makale a karkashin kwantin da ta fadi.

Advertisement

Da aka tuntubi Kwamandan sashin Aba, FRSC, mataimakiyar kwamandan rundunar, Jennifer Offor, ta ce rundunar ba ta da motar daukar kaya ko kuma crane, kuma dole ne ta dogara ga kamfanoni don samun motar da ta kwashe motocin da suka yi hatsarin a kan titin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending