News
Yan Majalisar Wakilai Sun Matsa Kaimi Don Kirkiro Sabbin Jami’oin Tarayya 32
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kimanin kudirori 32 ne aka gabatar a gaban majalisar dattawa da ta wakilai kan batun kirkiro sabbin jami’o’i da manyan makarantu kwalejoji Fasahada kwalejojin ilimi tun bayan kaddamar da majalisar dattawa ta kasa karo na 10, wani bincike da jaridar PUNCH ta gudanar ya nuna.
Kungiyar malaman jami’o’i da sauran masana, sun gargadi gwamnati kan kafa sabbin jami’oi da kwalejoji tare da gazawa wajen samar da kudaden da ake gudanar da su.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Najeriya na da jimillar jami’o’in gwamnatin tarayya 52. Bayanai daga hukumar kula da jami’o’in kasar sun kuma nuna cewa kasar na da jami’o’in jihohi 63 da jami’o’i masu zaman kansu 147.
Hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa ta kuma bayyana adadin makarantun kwalejojin fasaha na tarayya zuwa 40; mallakin gwamnatocin Jihohi guda 49 da masu zaman kansu 76. Akwai kwalejojin lafiya na tarayya da na jiha guda 70; yayin da adadin kwalejojin kiwon lafiya masu zaman kansu guda 17 ne.
Haka kuma, hukumar kula da kwalejojin ilimi ta kasa ta ce adadin kwalejojin ilimi a Najeriya 219.
Binciken da aka yi na kudurorin ya nuna cewa Shugaban Majalisar Wakilai ne ya jagoranci taron. Shugaban majalisar ya jajirce wajen ganin an kafa Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Kaduna, wadda ta yi karatun ta na farko a ranar 6 ga watan Yuli, 2023. Haka nan Mataimakin Shugaban Majalisar, Benjamin Kalu, ya matsa kaimi wajen kafa Jami’ar Federal University of Medical and Health Sciences Bende dake jihar Abia.
Akwai kuma kwalejin fasaha ta tarayya ta Benjamin Kalu, Rano, Jihar Kano; kwalejin fasaha ta tarayya, Shendam, Jihar Plateau, da dai sauransu.
Da yake zantawa da wakilin Jaridar Punch, Shugaban kungiyar ASUU na Jami’ar Tarayya ta Minna, Farfesa Gbolahan Bolarin, ya bayyana matakin da ‘yan majalisar suka dauka a matsayin wasu kura-kurai da suka sa a gaba.
