News
Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’i sun sanar da tsunduma yajin aiki a faɗin Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya ta tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani saboda rashin biyan ‘ya’yanta albashinsu na watanni huɗu a shekarar 2022.
Kwamitin haɗin guiwa na ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’in (JAC) a ƙarkashin jagorancin shugaban ƙungiyar ma’aikata ta SSANU, Mohammed Ibrahim, da Sakatare-janar ƙungiyar NASU Peters Adeyemi, ne suka tabbatar da ɗaukar wannan mataki a cikin wata sanarwa suka sanya wa hannu.
Zaɓen Kananan Hukumomi: Kungiyoyin Farar Hula 89 Sun Gabatar Da Rahoto Ga Hukumar KANSIEC
Ƙungiyoyin biyu sun ce za su fara wannan yajin aiki ne daga ranar Litinin 28 ga watan October a matsayin wani mataki na nuna halin ko-in-kula da gwamnatin tarayya take yi game da albashinsu na watanni huɗu da aka rike musu tun 2022.
Sakamakon haka, ƙungiyoyin suke umartar dukkan ‘ya’yansu da ke jami’o’i da sauran cibiyoyi da ke da alaƙa da su tsunduma yajin aikin kuma ka da su ba da ƙofa kowacce irin na tattaunawa da kowa.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
