Connect with us

News

Jirgi Ya Jefa Wa Masu Taron Mauludi Bom A Jihar Kaduna

Published

on

Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Wani jirgin soji ya jefa bom a kan masu taron Mauludi a yankin Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Aminiya ta gano cewa lamarin ya faru ne a misalin karfe 9 na daren Lahadi a yankin da ke kusa da Filin Jirgin Sama na Kaduna.

Ana Musayar Kalamai Kan Wakilan Najeriya dubu 1 da 411 A Taron COP23 A Birnin Dubai

Wani mazaunain yankin ya ce “mutane na cikin bikin Mauludi kawai sai jirgin sama ya jefo masu bom wanda ya yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 30 a wurin,” inji shi.

Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa akwai yiwuwar hasarar rayukan ya karu.

Advertisement

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ki bayyana yawan wayanda suka rasa rayukansu ba.

Amma ya ce za su sanar da manema labarai abin da ya faru a wurin bayan sun yi taron gaggawa na majalisar tsaron jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending