Connect with us

News

Gwamatin Tarraya na nazarin mika harkokin samar da wutar lantarki ga gwamnatocin jihohi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Gwamnatin tarraya na nazarin mikawa gwamnatocin jihohi hannayen jarinta a kamfanonin samar da wutar dake fadin kasar, domin sanya ido a kai da kuma tabbatar da cewar ana samun wutar yadda ya dace.

Yanzu haka gwamnatin Tarraya ke rike da kashi 40 na hannayen jarin kamfanonin samar da wutar guda 11 da ake kira DISCO, tun bayan mayar da su a hannun ‘yan kasuwa shekaru 10 da suka shude, yayin da kowanne guda ke samar da wutar a jihohi akalla 3 zuwa sama da haka.

Advertisement

Jerin Jahohin Arewacin Nijeriya Da Sojojin Nijeriya Suka Jefa Bama Bamai Bisa Kuskure

Ministan samar da wutar, Adebayo Adelabu ya bayyana wannan shirin, yayin da yace kofofinsu a bude suke ga gwamnatocin jihohin domin cimma yarjejeniya a kan wannan shirin.

Najeriya mai dauke da yawan mutane sama da miliyan 200, bata iya samarwa jama’arta yawan wutar da suke bukata domin gudanar da harkokin yau da kullum, matsalar da ta tilastawa wasu masana’antu rufewa domin komawa kasashen dake makotaka da kasar.

Advertisement

Library Radio ta ruwaito cewa Wannan matsala ta rashin wutar tafi illa ga masu kananan masana’antu wadanda suka dogara da ita domin gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Kokarin gwamnatin da ta shude ta shugaban kasa Muhammadu Buhari na gina tashar samar da wutar Mambilla wadda aka dade ana mahawara a kai ya ci tura, saboda abinda wasu suka kira zagon kasa daga wasu dake adawa da aikin.

Advertisement

Yanzu haka bankin raya kasashen Afirka na AfDB ya ware dala biliyan guda domin bunkasa tashoshin samar da wutar lantarki a wasu kasashen Afirka daga shekara mai zuwa, cikin su harda Najeriya.

A wani labarin kuma Jerin Jahohin Arewacin Nijeriya Da Sojojin Nijeriya Suka Jefa Bama Bamai Bisa Kuskure

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending