Connect with us

News

Da yuyuwar a sake fuskantar tafiya yajin aikin jami’oi a kasar nan a 2024

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Da yuyuwar a sake fuskantar tafiya yajin aikin jami’oi a kasar nan a shekara mai zuwa, sakamakon kason da aka ware masu cikin kunshin kasafin kudin shekara mai zuwa bai taka kara ya karya ba, kamar yadda kungiyar malaman jami’oi ta kasa ta baiyana.

Daily Post ta ruwaito cewa A hirarsa da manema labarai a jiya, Shugaban kungiyar na kasa, farfesa Emmanuel Oshodoke, Ya ce a yayin yakin neman zaben shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi alkawarin karawa kasafin fannin ilimi kimanin kaso 15 cikin 100.

CBN ya dakatar da cajin da bankuna ke yi wa kostomomi yayin ajiyar kuɗaɗe

Sai dai kuma y ace kungiyar ta baiyana mamakinta kan yadda aka warewa bangaren ilimi naira tiriliyan 2 da bilyan 18, wanda ya kama kaso 7 da digo 9 cikin 100 na kasafin kudin, kuma hakan ya saba ta tanadin hukumar bunkasa ilimi da raya al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO, wadda ta bukaci a rika warewa bangaren kaso 26 cikin 100.

Dagan an shugaban kungiyar malaman jami’oin ta kasa ya shawarci gwamnati da ta yi zama na musamman da ‘yan majalisar zartawa domin karawa fannin ilimi kaso mai tsoka a cikin kasafin kudi.

A Wani labarin kuma CBN ya dakatar da cajin da bankuna ke yi wa kostomomi yayin ajiyar kuɗaɗe

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending