News
‘Yan bindiga sun saki Mai Shari’ar Babbar Kotun Jiha, bayan ta kwana biyar a hannun su
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai Shari’a ta Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom ta samu kuɓuta daga hannun ‘yan bindiga, bayan ta shafe kwana biyar tsare cikin daji a hannun su.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ita a ranar Litinin, bayan sun bindige dogarin ɗan sandan da ke kare lafiyar ta.
Masu jiran a zartas masu da hukuncin kisa sun kai mutum 3,413 -Jami’in Kurkuku
‘Yan bindiga sun yi gaba da ita tare da direban ta, bayan sun bindige dogarin ɗan sanda mai kare lafiyar ta, kan hanyar komawa Uyo babban birni Jihar Akwa Ibom.
Justice Unwuna ta je Oron ne inda ya gudanar da shari’a. Ta yi gamo da ‘yan bindiga a cikin daji, waɗanda suka bindige dogarin ta, sannan su ka nausa cikin daji da ita da direban ta.
Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Akwa Ibom, Ini Ememobong ne ya sanar da kuɓutar mai shari’ar, tare da cewa Gwamna Umo Eno ya gode wa jami’an tsaro da suka kuɓutar da ita.
Sai dai kwamishinan bai bayyana ko sai da aka biya diyya kafin a sake ta ko ba a biya ba.
A ranar Talata PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa, bayan sace sarki da fadawa 22 a Taraba, ‘yan bindiga sun sungumi Mai Shari’a bayan sun bindige ɗan sandan da ke tsaron ta.
Yayin da al’ummar Jihar Taraba ke zaman zullumi da jimamin takaicin yadda ‘yan bindiga suka arce da wani basaraken jihar da fadawan sa 22, sai kuma ga shi wasu ‘yan bindiga sun arce da mai shari’a, sun yi garkuwa da ita, bayan sun bindige dogarin ɗan sandan da ke tsaron lafiyar ta.
Mai Shari’a a Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom, Justice Uwana ta faɗa hannun ‘yan bindiga waɗanda suka arce da ita ranar Litinin, kan hanyar ƙaramar hukumar Oron.
Haka nan kuma, a ƙoƙarin arcewa da ita sai da suka bindige ɗan sanda mai tsaron lafiyar ta har lahira.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, Odiko MacDon ya tabbatar da labarin yin garkuwa da babban mai shari’ar.
Ya ce Mai Ta haɗu da ‘yan bindiga lokacin da ta ke kan hanyar komawa Uyo, babban birnin jihar, bayan ta tashi daga zaman kotu a garin Oron.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa a baya-bayan nan wasu ‘yan bindiga suka sauke lodin makaɗa, mawaƙi, ‘yan rawa, ‘yan amshi da sanƙira, suka nausa da su cikin dokar daji.
Fitaccen mawaƙin ‘balaja’u’, rawar kwambilon da aka fi sani da kiɗan juju, Omoba De Jombo, ya faɗa hannun ‘yan bindiga, shi da ɗaukacin tawagar sa kakaf.
Sauran waɗanda aka yi garkuwar tare da shi, sun haɗa da dukkan tawagar da suka haɗa da ‘yan rawa, ‘yan amshi har ma da sanƙira.
An kama su ne kan hanyar su ta zuwa Kogi daga Abuja domin zuwa raƙƙashewa a Jihar Kogi.
Waɗanda suka yi garkuwa da su dai sun ce ba za su sake su ba sai an biya diyyar Naira miliyan 10 kan kowane mutum ɗaya.
Wani mawaƙi ne mai suna Adeyinka Adeboye ya fara watsa labarin yin garkuwa da tawagar ɗan uwan sa mawaƙin a shafin sa na Instagram, lamarin da ya ja hankulan jama’a da dama.
Boyebest ya ce masu garkuwar sun bugo waya, sun nemi a biya diyyar Naira miliyan 10 kan kowane mutum ɗaya.
Abokan sana’ar sa dai na ci gaba da muna damuwa da kuma addu’ar neman kuɓutar su.
Ya ce an kama su ne kan hanyar su bayan sun dawo daga Jihar Ondo, inda suka je suka yi wasa.
Wani mai suna Aysneakey ya bayyana cewa cikin waɗanda aka yi garkuwar da su, akwai ɗan’uwan sa ɗaya.
Ya ce an kama su ne tsakanin titin Obajana/Kabba.
Sai dai kuma ba a bayyana yawan waɗanda aka yi garkuwar da su ba. Kuma ba a bayyana jinsin ‘yan bindigar da suka arce da su ba.
Haka kuma har zuwa yanzu ba a san shin har da kayan kiɗan aka haɗa aka nausa cikin daji da su ba, ko kuma a cikin mota aka bar kayan kiɗan.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
