News
Yan bindiga sun kashe wasu mutane a Nijar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Mutum goma sha daya ne suka mutu a hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyuka biyu na Jamhuriyar Nijar da ke kan iyaka da Burkina Faso a karshen mako, a cewar sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ranar Lahadi.
“’Yan ta’adda a kan babura da dama sun kai hari a kauyukan Amara da Loudji,” masu nisan kilomita 30 a kudu maso gabashin Bankilare, “inda suka kashe mutum 11,” in ji sanarwar.
Yan Sanda Sun Kama Barayin Gadajen Daliban ‘Unity School’ a Jihar Jigawa
Sun kai harin ne a yayin da jami’an tsaron Nijar suka “kaddamar da jerin hare-hare” ranar Juma’a, wadanda ma’aikatar tsaron ta ce “sun lalata daukacin” hanyoyin sadarwar ‘yan ta’addan.
Ta kara da cewa an kashe soja daya tare da jikkata guda biyar ranar Juma’a lokacin da motarsu da ke yin sintiri ta taka nakiya a kauyen Ouro Gueladjo, mai nisan kilomita 70 daga Yamai, babban birnin kasar.
Tun daga watan Yuli sojoji suke mulki a Nijar bayan sun kifar da gwamnatin farar-hula.
Ranar 17 ga watan Disamba, shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya ce kasar tana “samun ci-gaba” wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa sojoji sun samu “nasarori da dama” ta hanyar dakile tarzoma.
Sojoji da mazauna yankunan da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali sun ce an samu kwanciyar hankula a makonnin da suka gabata.
A watan Oktoba an kashe sojoji shida a kan iyakar Nijar da Burkina Faso sakamakon ba-ta-kashi da ‘yan bindiga.
Kazalika a watan na Oktoba, an kashe sojojin Nijar 29 a hari mafi muni da ‘yan bindiga suka kai musu tun bayan juyin mulkin da soji suka yi.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
