Connect with us

Sports

An ci tarar Gombe United miliyoyi tare da zabtare mata maki uku

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

An tuhumi kungiyar kwallon kafa ta Gombe United da laifin karya dokokin NPFL bayan rashin samar da ingantaccen tsaro a wasansu na ranar Lahadi 17 da Rivers Utd.

Rashin tabbatar da ingantaccen tsaro da kungiyar Gombe Utd ta yi ya haifar da tarzoma bayan kammala wasan, inda magoya bayanta suka rika jefa abubuwa a cikin filin wasa da kuma cin zarafin jami’an wasan bayan kammala wasan.

Advertisement

’Yan bindiga sun sace matafiya 30 a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. 

Shima babban kociyan kungiyar Gombe Utd Mohammed Baba Ganaru an tuhume shi da tunzura magoya baya wajen cin zarafin jami’an wasan.

Wiki time ta ruwaito cewa An ci tarar Gombe Utd Naira miliyan 1 kan laifin rashin samar da isasshen tsaro sannan kuma an ci tararta Naira miliyan 1 kan laifin jefa abubuwa a filin wasa.

Advertisement

Sannan za a cirewa Gombe Utd maki 3 da kuma kwallaye 3 daga makinsu da suka tara sakamakon cin zarafin jami’an wasan.

Haka kuma an dakatar da babban kociyan kungiyar ta Gombe Utd, Mohammed Baba Ganaru daga wasanni 3 masu zuwa. Kuma mawa dai An ci tarar Naira miliyan 1 ga Gombe Utd bisa laifin rashin da’a da zai iya bata sunan wasan.

Advertisement

Gombe Utd za ta kuma biya tarar N500,000 a matsayin diyyar ga alkalin wasa Sa’id Abdul’Aziz da mataimakin alkalin wasa Cletus Adewebi (N250,000 kowannensu).

Gombe Utd za ta buga wasansu na gaba a gida a filin wasa na Pantami ba tare da magoya baya ba kafin hutun tsakiyar kakar wasanni. Haka Gombe Utd tana da sa’o’i 48 domin daukaka kara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending