Sports
An ci tarar Kano Pillars Naira miliyan 10
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An ci tarar Kano Pillars Naira miliyan 10 saboda jinkirin da kawo tsaiko wajen haska wasa kai tsaye a wasan su da Plateau Utd ranar Lahadi.
Kano Pillars za ta biya tarar Naira miliyan 1 kan laifin jefa abubuwa da dama a cikin fili da kuma wata Naira miliyan 1 kan nuna rashin da’a da zai iya jawowa wasan abun kunya.
Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Fatattaki Shugabannin FCCPC, BPE
Sannan za su biya tarar N250,000, a matsayin diyya, ga mataimakin alkalin wasa Sodiq Adejumo kan raunin da ya samu.
Kungiyar za ta buga wasanninta na gida (filin wasa na Sani Abacha) a nan gaba ba tare da magoya baya ba daga nan har zuwa hutun rabin kaka.
Kungiyar na da sa’o’i 48 daga lokacin sanarwar domin daukaka kara.
A wani labarin kuma Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Fatattaki Shugabannin FCCPC, BPE
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
