Connect with us

Sports

Guinea ta danƙara wa Super Eagles kwallaye biyu a raga, bayan kurin lallasa Al-Gharib 12-0 da ta yi

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

 

Bayan lallasa kungiyar kwallon kafa ta Al-Gharib 12-0 Super Eagles sun sha kashi a wurin kungiyar Guinea da ci biyu babu ko ɗaya.

Wannan rashin nasara ya tasa wa ƴan Najeriya hankali ganin kwanaki kaɗan ya rage a fara wasan cin kofin nahiyar Afrika.

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Fatattaki  Shugabannin FCCPC, BPE

Guinea ta jefa kwallon farko a minti na 14 da fara wasa, lamarin da ya dagulawa ‘yan wasan Najeriya lissafi, sannan Moses Simon ya kashe wata dama ta bugun fanareti, inda a minti na 19 da fara wasa. Golan Guinea ya buge Simon.

Premium Times ta ruwaito cewa Bayan Eagles na farko da Equatorial Guinea a ranar 14 ga watan Janairu, Super Eagles za ta kara da Giwayen Cote d’Ivoire a ranar 18 ga watan Janairu, kafin wasan karshe na rukuni na karshe da Wild Dogs na Guinea-Bissau a ranar 22 ga Janairu

Advertisement

A wani labarin kuma Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Fatattaki  Shugabannin FCCPC, BPE

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending