Connect with us

Sports

Shugaba Tinubu ya amince a biya Super Eagles da wasu ‘yan wasan Nijeriya bashin biliyan 12

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin wasannin Nijeriya suke bi, daga ciki har da kungiyar Super Eagles.

Daga cikin bashin da za a biya, har da kudaden da manyan kociya ke bi na albashinsu wanda ya kai watanni 15. Haka kuma akwai alawus-alawus da kuma alkawura da aka yi wa manyan ‘yan wasa maza da mata da ‘yan kasa da shekara 20.

Advertisement

An kama wani matashi da ake zargi da laifin daba wa mahaifinsa wuka har lahira a Kano

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babbar kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles ke shirin soma wasa a gasar AFCON wadda za a fara a cikin watan nan na Janairu.

Tun a bara sai dai kungiyar ta Super Eagles ta yi barazanar kin buga gasar ta AFCON kan kin biyanta hakkokinta.

Advertisement

Masu sharhi dai sun sha danganta rashin rashin karsashi da a wasu lokuta ‘yan wasan na Nijeriya ke nunawa a wasannin nasu da rashin biyansu hakkokinsu da suka dace wanda hakan ke kara sanyaya musu gwiwa.

 

Advertisement

TRT Afrika

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending