News
Babbar Magana: Bakuwa Ta Sace Jariri Awa 3 Da Haihuwarsa A Asibiti A Jihar Nasarawa.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wata mata ta sace jariri awa uku bayan haihuwarsa a Asibitin Kwararru na Dalhatu Arafat (DASH) da ke garin Lafia, Jihar Nasarawa.
Ana zargin bakuwar ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon sa’o’i kadan da haihuwarsa ta hanyar yi wa mahifiyarsa tiyata.
Badakalar Kudi: EFCC Ta Kwace Fasfo Din Betta Edu Da Sadiya Farouk Domin Hana Su Guduwa.
Aminiya ta ruwaito cewa bayan haihuwarsa da misalin karfe 3 na asubahin ranar Talata ne jami’an asibiti suka mika jaririn da mai jegon ga wata ’yar uwarta domin ta ci gaba da kula da su.
Wani ganau da ya nemi a boye sunasa ya ce, bayan sun dawo dakin masu jego ne ’yar uwar mai jegon ta kawo mata da wata bakuwa, wadda ake zargin sun hada baki wajen sace jaririn.
‘Kamar Layar Zana’
A cewarsa, “’yar uwar mai jegon ce ta ce mata za ta koma gida ta dauko cajar wayarta da ta manta; shi ne ta hada ta da wata mata da za ta zauna da su kafin ta dawo ,” wadda ake zargin ita ce ta sace jaririn.
Sace jaririn daga dakin masu jegon da misalin karfe 6 na safe, awa uku da haihuwarsa ya jefa daukacin jami’ai da sauran mutanen asibitin cikin al’ajabi.
Wata ’yar uwar mai jegon da ta nemi a boye sunanta, ta tabbatar cewa, ’yar uwarsu ce kawo wa mai jegon wata bakuwa, ta kuma damka mata jaririn.
A cewarta, ba su yi aune ba, sai dai aka nemi jaririn da bakuwar — wadda ya yi zargin matsafiya ce — suka rasa, sun yi layar zana.
Ta ce, “Ba mu ga barauniyar jaririn ba, wannan wane irin rashin imani ne, mace ta shiga asibiti ta yaudari duk ’yan dakin da masu tsaron kofa cewa za ta yi masa wanka, amma ta tsere da jariri. Duniya ta zama abin tsoro!”
Yadda Aka Sace Jaririna —Mai Jego
Mai jegon, Malama Wasira Suleiman, wadda ke zubar da hawaye, ta ce “wadda aka kawo domin ta taimaka wajen kula da jaririn, ita ce ta sace jaririn da na dauka a cikina wata tara.”
Malama Wasira ta roki Gwamnatin Jihar Nasara da hukumar gudanarwar Asibitin DASH da hukumomin tsaro su taimaka su ceto jaririn nata ba tare da komai ya same shi ba.
Mahaifiyar jaririn ta bayyana cewa, “saboda ba ni da karfin da zan iya yi wa kaina komai” aka kawo matar a matsayin ’yar aike — idan mai jegon tana bukatar wani abu, ko sayen magunguan idan an bukaci hakan.
A cewarta, bayan an bar matar ce ta bukaci yi wa jaririn wanka, amma ta ce ta bari sai ’yar uwarta ta kawo kayansa.
Amma duk da haka matar ta nace cewa tana da kayan da za a lullube shi idan aka yi wankan, a karshe da mai jegon ta amince matar ta yi masa wanka, sai daga baya aka ce mata a sace jaririn nata.
“Wahalar da na sha na wata tara ba shi da misali, don haka babu abin da za a fada min da zan hakura; karfe biyun dare aka yi mini tiyata fa,” in ji mai jegon.
Bai Taba Faruwa Ba —Hukumar Asibiti
Mukaddashin Shugaban Sashen Kula da Masu Juna Biyu na Asibitin DASH, Dalhatu Arafat ya bayyana takaicinsa kan lamarin yana mai cewa haka bai taba faruwa a asibitin ba.
A cewarsa, bayan an yi wa mai jegon aiki ta haihu da misalin karfe 3 na asubahin Talata aka kai ta dakin masu jego tare da mai kula da it.
Ita kuma ta kawo wata bakuwar da ba ta sani ba domin kula da su, za ta je gida ta dauko wani bu.
“Abin takaici, bakuwar ta dauki jaririn da cewa za ta yi masa wanka, daga nan ta yi layar zana da shi, abin da mu a asibitin muka sani ke na,” in ji shi.
Amma ya ce duk wadanda ke da alaka da sace jaririn sun hannun ’yan sanda ana bincike domin gano bakuwar da ta sace jaririn.
Dalhayu Arafa ya ce, “sai da muka kira kowa, saboda wannan ne karo farko a haka ya faru a nan” kuma wadanda aka kama sun hada da ’yar uwar mai jegon da ta kawo bakuwar da wasu ma’aikatan asibitin da ke aiki a lokacin da abin ya faru.
Duk wanda aka samu da hannu za mu sallame shi mu mika shi ga hukuma, domin zama darasi ga masu irin wannan hali.
“Za kuma mu kara amfani da kyamarorin CCTV domin daukar duk wani motsi a cikin dakunan marasa lafiya,” in ji shi.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
