News
Wata Sabuwa: Ƙungiyar Ƙwadago ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnati
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata gaggarumar tarzomar yajin aiki ta kunno kai a jihar Kwara yayin da kungiyoyin kwadago suka bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar kan rashin biyan bukatunta.
Bukatun, a cewar Murtala Saheed Olayinka, Tunde Joseph da Saliu Suleiman, shugabanin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC a jihar, sun hada da rashin aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 35 biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
‘Yan bindiga sun bukaci a biya diyyar naira miliyan 50 kan tsoho mai shekaru 70 da suka kama
Daily Post ta ruwaito cewa A wani taron manema labarai da suka gudanar a Ilorin, kungiyar kwadagon ta kuma koka kan kin amincewa da gwamnatin jihar na ƙin aiwatar da kashi 40 cikin 100 na alawus alawus kamar yadda gwamnatin tarayya ta amince.
Sauran bukatu sun hada da biyan ’yan fansho da aka yi musu gyara tun bayan amincewa da sabon mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta yi a shekarar 2019 da kuma rashin biyan ma’aikatan kananan hukumomin basussukan da suke bi.
Ƙungiyar ta kuma yi Allah wadai da rashin isassun kudade na manyan makarantun jihar, da rashin son daukar ma’aikatan Otal din Kwara ba tare da wani sharadi ba da kuma rashin sanya ma’aikatan kamfanin ruwa da aka sake tura su cikin babban ma’aikatan jihar ta Kwara.
Kungiyar kwadagon ta ce dole ne ta bayar da wa’adin ganin yadda gwamnatin jihar ta ki amincewa da bukatar ma’aikatan gwamnatin jihar, wanda hakan ya sanya fargabar zaman lafiya da kwanciyar hankali a masana’antu.
