Connect with us

News

Hukumar NSCDC ta kama mahaifin da ya yi kokarin sayar da dansa mai shekaru 6 a kan N20m

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, ta cafke wani da ake zargi mai suna Chinana Tali bisa zargin safara da yunkurin sayar da dansa mai shekaru shida a kan kudi Naira miliyan 20 a Abuja.

Kwamandan NSCDC babban birnin tarayya, Olusola Odumosu, ya tabbatar wa manema labarai haka a ranar Talata, inda ya ce an kama wanda ake zargin ne a wurin siyar da shi bayan an kama a hanyar zuwa Abuja daga Benue.

Dalilin da ya sa AS Roma ta zabga wa Jose Mourinho takardar sallama

Kamfanin Dillancin Labarai Na Kasa NAN ya bayar da rahoton cewa, wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi a ofishin hukumar NSCDC ta FCT ya yi ikirarin cewa wanda aka kashen Ushafa Tali dan sa ne mai shekara shida a duniya.

Tali ya bayyana cewa shi uba ne mai ‘ya’ya shida kuma ya yanke shawarar sayar da daya daga cikin ‘ya’yansa ne domin ya taimaka wajen samun kudi don kula da dimbin iyalinsa.

“Saboda wahala ne kuma babu kudi, don haka ina bukatar in sami hanyar horar da sauran ‘ya’yana,” in ji Tali.

Advertisement

Kwamandan Hukumar NSCDC ya lura cewa kama mahaifin da ke tare da dansa ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu na kokarin mahaifin na neman farashi mai kyau a kan yaron.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending