News
Yanzu-yanzu: Wani Abu Ya Fashe A Tashar Iskar Gas A Ibadan
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Wani mummunan abu ya fashe a wata fitacciyar tashar iskar gas a unguwar Sango da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa, fashewar ta razana mazauna garin, inda suka shiga firgici suna neman wurin tsira.
Hukumar NSCDC ta kama mahaifin da ya yi kokarin sayar da dansa mai shekaru 6 a kan N20m
An ji karar ne da misalin karfe 8:00 na dare, inda karar ta kai sassan birnin Ibadan har zuwa Bashorun da Amuda Ojeere da ke kan babbar hanyar Legas/Ibadan.
Shahararriyar Kasuwar Ace Mall wacce ke da shahararren gidan sinima na Ventura a Samonda da ke da nisan wasu ‘yan daruruwan mitoci daga wurin da abin ya faru, sai da wani bangaren ginin ya ruguje sakamakon karar, acewar mazauna yankin.
Har yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu ba da wadanda suka jikkata zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.
