News
Kotun koli ta tabbatar da Abdullahi Sule a matsayin gwamnan Nasarawa.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotun koli ta ayyana Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Nassarawa.
Kotun dai ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP David Umbugadu ya shigar inda yake kalubalantar nasarar Abdullahi Sule.
Kwamitin alkalai ya yanke hukuncin bai daya inda ya kori ƙarar saboda rashin cancanta.
Advertisements
