Connect with us

Politics

Da alama siyasar Jihar Kano na shirin sake zani

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Wata dambarwar siyasa ta kunno kai a jihar Kano, inda ake ganin wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar, ciki har da masu rike da mukamai, suna tattauna yiwuwar canza shekar tafiyarsu ta Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan hukuncin kotun ƙolin ƙasar wanda ya bai wa gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf, nasara a wata shari’a kan halascin zaɓensa.

Super Eagle Zata Fafata Da Kamaru A Gasar AFCON A Zagaye Na 16

A halin da ake ciki dai babu ga-maciji tsakanin Jagoran tafiyar siyasar Kwankwasiyya wato Rabi’u Musa Kwankwaso, da Abdullahi Umar Ganduje, shugaban riƙo na jam’iyyar APC kuma jagoran jam’iyyar a Kano.

Batun dai ya soma ƙamari ne bayan an jiyo gwamna Abba Kabir Yusuf, na ta godewa shugaba Bola Tinubu bayan hukuncin da kotun ƙolin Najeriyar ta yanke, da ya tabbatar da halascinsa a matsayin gwamna, duk da zarge-zargen da ya sha yi a baya na cewa ana shirya wata maƙarƙashiya domin ƙwace kujerar tasa.

Advertisement

Kwatsam kuma sai aka ga bullar wasu rahotanni da ke cewa shugaba Bola Tinubu ya ba wa jagororin jam’iyyar ta APC umarnin su je su sasanta da jagoran jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso, aka kuma fara ganin wasu mashawartan Gwamna Abba suna sanye da huluna masu ɗauke da tambarin hular Shugaba Tinubu, har wasu ma sun kai ga sanya tutar jam’iyyar APC a ofisoshinsu.

Injiniya Buba Galadima, na cikin shugabannin jam’iyyar NNPP na Najeriyar, ya kuma yi wa BBC bayanin cewa a siyasance jam’iyyar na iya tattaunaa da kowanne ɓangare, ‘ ‘Yan NNPP da suka fara sanya alamun jami’iyyar APC, ƙlia sun zaƙu ne na cewa a yi tafiya tare, amma wanna bai nuna cewa su ne ke riƙe da jam’iyya ko suke riƙe da gwamnati wanda za su iya zartarwa ba’. In ji shi

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending