Connect with us

News

Hukumar INEC ta dakatar da zaɓen cike gurbi a Kano da Enugu da Akwa Ibom

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC sanar da dakatar da zaɓukan cike giɓi da ake gudanarwar a jihohin Kano da Enugu da Akwa Ibom.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon matsalolin da aka samu na satar da kayan zaɓe da yin garkuwa da wasu jami’an zaɓe a jihohin.

Advertisement

Sadakin aure yayi tashin Gauron zabin da baitaba yiba a Nigeria

Sanarwar ta ce wuraren da lamarin ya shafa sun haɗar da mazaɓar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, inda INEC din ta ce aka samu wasu ɓata-gari suka lalata kayan zaɓen.

A jihar Enugu kuwa da ke kudu maso gabashin ƙasar, hukumar zaɓen ta ce an fitar da takardun sakamako tun kafain fara zaɓe.

Advertisement

A ƙananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa kuma, INEC din ta ce an samu hatsaniya a rumfunan zaɓe 10, inda ‘yan daba suka lalata kayan zaɓe tare da hana gudanar da zaɓen.

Hukumar zaɓen ta ce ta yi aiki da sashen dokar zaɓen na 24 wajen dakatar da zaɓen.

Advertisement

Hukumar ta kuma yi kira ga jami’an tsaro da su gudanar da bincike kan lamurran, inda hukumar ta ce tana gudanar da cikakken bincike daga nata ɓangare, don gano ko jami’anta sun saɓa doka a ayyukansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending