Connect with us

News

Sadakin Aure Yayi Tashin Gauron Zabin Da Baitaba Yiba A Nigeria

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Kwamitin dake kula da ganin watan hadi da harkokin nisabin zakkah da na sadakin a Najeriya ya ce mafi ƙarancin kuɗin sadaki a Najeriya ya koma 99,241.

Cikin wata sanarwar da kwamitin ke wallafawa a kowace rana a shafukansa na sada zumunta ya nuna cewa a yanzu mafi ƙarancin kudin sadakin shi ne 99,241.

Advertisement

Zoben bakin karfe kadai ya wadatar a matsayin Sadaki -malam ibrahim 

Ƙaruwar kuɗin sadakin ba ya rasa nasaba da faɗuwar darajar kuɗin Najeriya, wani abu da ke ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mummunan hali.

Shi dai kuɗin sadaki ana lissafa shi da darajar zinare da azurfa a kasuwannin duniya.

Advertisement

A watan da ya gabata mafi ƙarancin sadaki a ƙasar bai haura naira 70,000 ba.

Yadda ake ƙayyade sadaki mafi ƙaranci da nisabin Zakkah da haddin sata da dai sauransu a musulunci

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending