News
Zoben bakin karfe kadai ya wadatar a matsayin Sadaki -malam ibrahim
DAGA WAKILIN MU B.IMAM
Shugaban majilisar malamai ta jihar kano malam ibrahim khalil ya ce zoban bakin karfe kadai ya wadatar a matsayin Sadakin aure.
Malam Ibrahim ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da wakilin Jaridar Inda Ranka a jihar Kano
Shugaban Karamar Hukuma A Kano Ya Yi Murabus, Wani Kuma Ya Fice Daga APC Zuwa NNPP
Ya bayyana cewa da yawan mutane basu fahimci mai ake nufi da sadaki ba inda yake bayyana cewar shi sadaki Musulunci ya shirya shi domin amarya ta samu abin da za ta yi hidim haka kuma qsadaki ba na iyaye ba ne, hakkin amarya ne.
Matar da za’a aura koda cewa tayi ta yafe sadakin batai laifi ba amma zaka ji ana cewa wai aure bai dauru ba muddun ba’a kai kiyasin da aka kiyasta ba
Malamin yace a zamanin shugaban halitta wani bawan Allah yazo neman aure amma bashi da komai sai mayafin sa in kuma ya rabashi biyu bazai ishe kowannen suba sai shugaban halitta yace yaje ya samo ko menene inda kuwa ya samo zobe na bakin karfe dashi kuwa aka sahale masa auran wanan mata
A karshe yayi kira ga malamai da limamai dasu daina cewa sai dole kudin sadaki yakai nusabi
