News
An cafke matar da ta sayar da yara sama da 42
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata ’yar shekara 45 mai suna Alimot Haruna mai fataucin kananan yara, ta bayyana cewa ta sayar da yara sama da 42 a cikin shekaru biyar da suka gabata.
A ranar Laraba ne wata tawagar ’yan sanda daga ofishin ’yan sanda na Ijora Badia na rundunar ’yan sandan Legas ta cafke wadda ake zargin.
Hukumar EFCC ta tsare ƙanin Hadi Sirika kan binciken badaƙalar N8bn
An tattaro cewa wadda ake zargin wanda cibiyarta ke a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta kasance cikin jerin sunayen ’yan sandan da ake nema ruwa a jallo kan irin wannan laifin.
Wadda ake zargin a cikin sanarwar da ta yi na ikirari ta ce tana gudanar da aiki ne daga sansaninta da ke kauyen Molete a jihar Kwara.
“Na sayar da yara sama da 42 ga abokan ciniki daban-daban a baya. Yawancin abokan cinikina suna zaune ne a Legas.”
“Manufana yara ne tsakanin shekaru 7 zuwa 12. Ina kawo yaran Legas domin aikin yara,” inji ta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da kamen, ya ce an kubutar da kananan yara uku masu karancin shekaru daga hannun wadda ake zargin.
Hundeyin ya ce daga karshe an kama wanda ake zargin wanda shi ne shugaban wata kungiyar fataucin yara bayan watanni uku ana bincike na gaskiya.
Ya ce rundunar ta dade tana bin kungiyar tun lokacin da ta samu bayanai kan ayyukanta.
“A ranar 25 ga Janairu, 2023, da misalin karfe 5:45 na yamma, jami’an tsaro da ke sa ido kan motsin ta sun kama shugaban kungiyar Alimot Haruna na kauyen Molete a Ilorin, jihar Kwara. Ana cikin haka ne, yara uku ’yan kasa da shekaru biyu, mace biyu da namiji daya da ba a iya tantance sunayensu ba, wadanda shekarunsu suka kai 12 da 7 babu wani takamaiman adireshi da aka ceto daga hannunta.
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa. Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya kawo yara sama da 52 Legas ba bisa ka’ida ba domin yin aikin yara ba tare da izinin iyayensu ba.
“An kuma bayyana cewa rundunar ’yan sandan jihar Kwara ta bayyana wanda ake zargin a kan bacewar wasu kananan yara da ba su kai shekaru ba. Dukkan yaran da suka bace dai rundunar ’yan sandan jihar Kwara ce ta alakanta su da kungiyar ta Anti-Humab.
