News
Hauhawar farashi ba za ta ragu ba sai Najeriya ta rage kayan da take bukata daga waje’ —Gwamnan CBN
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Babban bankin Najeriya CBN Olayemi Cardoso ya bayyana cewa kasar ba za ta rabu da matsalar karancin dala da hauhawar farashi ba sai ta kara yawan kayan da take fitarwa zuwa kasashen waje, maimakon shigar da mafi yawan kayan bukata da ake yi a halin yanzu.
Gwamnan na CBN ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da ya amsa gayyatar da majalisar wakilan kasar ta yi masa domin yin bayani kan hauhuwar farashin kayan masarufi da karancin takardar kudin dala da kasar ke fama da shi.
Darajar naira dai na ci gaba da faduwa idan aka kwatanta da dalar Amurka, lamarin da ke kara iza wutar matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar.
Sai dai a lokacin da ya bayyana gaban majalisar, Cardoso ya ce Babban bankin kasar da wasu hukumomi daban-daban na daukar matakan da za su taimaka wajen rage hauhawar farashi da daga darajar naira nan ba da dadewa ba.
Gwamnan babban bankin Najeriya Olayemi Cardoso da ministan kudi da kuma ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Senata Atiku Bagudu da shugaban hukumar tattara kuddade shigar Najeriyar sun shafe kusan sa`a shida suna amsa tambayoyi daga `yan majalisar wakilai a kan faduwar darajar naira da tsadar rayuwar da ake fama da ita a kasar, inda jami`ai daga bangaren zartarwa suka nuna cewa gwamnatin tarayyar tana sane game da mawuyacin halin da `yan kasa ke ciki….kuma tana daukar matakai daban-daban don rage wa al`umma kuncin da suke ciki.
Sai dai sun bayyana cewa da wuya a yi bankwana da matsalar tasadar dala sai masana`antu sun bunkasa ta yadda za a dinga fitar da ake samarwa a gida ana ka iwa waje.
