News
Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Yi Wa Gwamnonin PDP Raddi Akan Matsalar Tattalin Arziki
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnantin Tarayya ta maida wa Gwamnonin PDP raddi, bayan sun kwatanta halin da tattalin arzikin Najeriya ya ke ciki da irin na ƙasar Venezuela.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya ce duk da dai tattalin arzikin Najeriya na fuskantar ƙalubale, kwatanta shi kafaɗa-da-kafaɗa da na Venezuela da gwamnonin PDP suka yi, rashin adalci ne ainun.
‘Yan majalisun Najeriya sun bukaci komawa tsarin mulkin Firaminista
“Muna bayyana cewa duk da ƙasar mu na fuskantar wasu matsaloli, waɗanda kuma wannan gwamnati ta Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin magance su, to kuma matsalolin mu ko kusa ba su kai ga na Venezuela ba, kamar yadda gwamnonin PDP suka rufe ido suka faɗa,” haka Idris ya bayyana a cikin wata sanarwar da aka raba wa PREMIUM TIMES a ranar Talata.
“Tattalin arzikin Najeriya har yanzu ya na da ƙarfi sosai, kuma ana sa rai da kyakkyawan hasashen cewa zai bunƙasa da ƙarin kashi 3% bisa 100% cikin wannan shekarar.
“Tattalin arzikin mu na bayar da gudunmawar lamuni ga masu ramce a cikin gida da waje.”
A ranar Litinin ce dai gwamnonin PDP suka gudanar da taro a Abuja, inda suka tattauna batutuwa, musamman waɗanda suka shafi matsalar tsaro da matsalar tattalin arziki, wadda ta haifar da matsalar tsada da raɗaɗin tsadar rayuwa.
Bayan kammala taron, sun bada sanarwar cewa sun amince kowace jiha a ba ta damar kafa ‘yan sandan jiha, domin a samu a shawo kan ƙalubalen matsalar tsaro a faɗin ƙasar.
Minista Idris ya ce muna maraba da shawarwarin da suka bayar waɗanda ba na son rai ba, domin ganin an magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki,” inji Idris.
Daga nan kuma ya fara ragargazar gwamnonin da cewa sun taimaka wajen haifar da matsalar tattalin arziki.
“A matsayin su na shugabanni a gwamnatocin jihohi, gwammonin PDP su na da ‘yancin bayyana matsayar su kan duk wani abu da ya shafi ƙasar nan.
“To sai dai mambobin Majalisar Tattalin Arziki da kuma Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, mun yi amanna da cewa gwamnonin ba su nuna dattakon da ya kamata su nuna ba, a matsayin mu na shugabannin jama’a.
“A matsayin gwamnonin PDP, waɗanda ya kamata a ce masu shiga sahun gaban inganta tattalin arziki ne, samar da yalwa a ƙasa ga ‘yan ƙasar a jihohin su, a ce kuma sun koma su na furka kalaman ƙage da shaci-faɗi kan Najeriya, har su na kwatanta matsalar tattalin arzikin Najeriya da irin matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin Venezuela.
“Mu na son mu bayyana cewa duk da dai tattalin arzikin mu na fuskantar ƙalubale, amma ki kusa ba daidai ba ne a kwatanta matsalar Venezuela da ta Najeriya.
“Yayin da gwamnatin tarayya ke biyan albashi da sauran haƙƙoƙin ma’aikata kan kari, kuma harkokin gwamnati na tafiya daidai-wa-daida, ya kamata ‘yan Najeriya su tambayi gwamnonin PDP abin da suka yi da kuɗaɗen da ake ba su. Saboda akwai rahoton bincike mai nuna cewa yawancin jihohin PDP sun kasa biyan ‘yan fansho kuɗaɗen su na tsawon watanni da dama, haka albashin ma’aikata ma wasu ba su biya yadda ya kamata. Gwamnonin PDP na ƙin biyan garatutin ma’aikatan da suka yi ritaya.
“Haka kuma wasu gwamnonin PDP ɗin har yau sun kasa ma biyan Naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, shekaru huɗu da gwamnatin tarayya ta fara amfani da tsarin,” inji Minista Idris.
