Connect with us

News

Shirin Agile A Kano Zai Hada Hannu Da Masu Ruwa Da Tsaki A Makoda Domin Ci Gaba Da Inganta Ayyuka

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Shirin AGILE a jihar Kano zai ci gaba da shigo da masu ruwa da tsaki domin sake bunkasa shirin ta hanyar amfanar da al’ummar birni da kuma karka.

Wannan na zuwa ne bayan wata ziyara da tawagar shirin na AGILE ta kai karamar hukumar Makoda a nan Kano, domin ganawa da masu ruwa da tsaki don sake nuna muhimmancin hadin gwiwa wajen bunkasa shirin ayyukan shirin.

Advertisement

A Shirye Nake Na Aure Murja Kunya — Ibrahim Assalafi

Matakin na zuwa ne domin shigar da masu ruwa da tsaki na cikin gida, musamman shugabannin al’umma, da jami’an gwamnati, Sarakuna da kuma Malamai duka domin sake bunkasa Shirin.

Ana saran Wannan hanya za ta haɓaka ci gaba Da bayyana gaskiya, haɗa kai, da fahimtar alaka tsakanin masu ruwa da tsaki, tare da haɓaka tasirin ayyukan shirin a ko ina.

Advertisement

Bugu da kari, yin cudanya da masu ruwa da tsaki na bai wa shirin AGILE a Kano damar yin amfani da ilimin cikin gida da gogewa, wanda zai kai ga samar da ingantacciyar shawara da kyakkyawan sakamako ga al’umma.

Wakilan shirin na AGILE din sun kuma tabbatar da yin duk abin da ya dace, da tsarin haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da ke da mahimmanci don ilimantar da Al’umma a karamar hukumar Makoda dama jihar Kano baki daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending