Business
Gwamnatin Tarayya Na Tattaunawa Da Banin Duniya Domin Samun Lamunin Sama Da Dala Biliyan 1
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarayyar Najeriya na tattaunawa da bankin duniya domin kammala shirye-shiryen samun lamunin sama da dala biliyan 1 domin magance kalubalen da ‘yan gudun hijirar ke fuskanta da kuma al’ummar da suke zaune, tare da karfafa hanyoyin shiga yankunan karkara da kasuwancin noma a kasar.
Bukatar tana kunshe ne a cikin wani daftarin bankin duniya na baya-bayan nan mai taken, ‘Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project’ da kuma ‘Rural Access and Agricultural Marketing Project – Scale Up.’
Dangane da haka, yayin da ake ba da lamuni na ‘yan gudun hijirar kan dala miliyan 500, an kiyasta rancen hanyoyin shiga yankunan karkara da kuma tallata aikin gona a kan dala miliyan 550.
Daily Post ta ruwaito cewa Ana sa ran asusun zai ba da taimako ga al’ummomin Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro.
“Aikin da aka tsara zai yi amfani da hanyoyi uku don samar da mafita mai dorewa ga ‘yan gudun hijira da mazauna yankin Arewacin Najeriya.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
