News
Mutane 10 ne suka mutu, 48 suka jikkata a wani hatsarin tirela a hanyar Abuja zuwa Kaduna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu 48 suka samu raunuka daban-daban a lokacin da wata motar tirela ta DAF ta afka cikin wani rami da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Hadarin wanda ya afku da misalin karfe 10:30 na safe ya rutsa da manya maza 172, kamar yadda kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), mataimakin shugaban hukumar Marshal ya bayyana.
Hukumar EFCC Ta Kwato Gidaje 324 Na ‘Yan Fansho Da Aka Karkatar A Jihar Kano
Hakan na kunshe ne ta cikin Sanarwa da Jonas Agwu, ya fitar a ranar Talata, 19 ga watan Maris.
Ya ce: “Hatsarin da ya hada da Tirelar DAF ya faru ne sakamakon wuce gona da iri hakan ya sa direban ya sassauta sarrafa ƙafafun ta yadda ya fada cikin wani rami da ke kan hanyar.”
“Ya zuwa lokacin gabatar da wannan sanarwa, tawagar ceto FRSC ta kammala kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitocin Saint Anthony da Umaru Musa ‘Yar Adua yayin da fasinjojin da Suka Mutu kuma aka ajiye su a dakin ajiye gawa na asibitocin da aka ambata.
“Har yanzu ana ci gaba da kokarin jami’an FRSC na bin diddigin wadanda suka jikkata a asibitoci domin ganin sun samu kulawar da suka dace.”
