Connect with us

News

Kwamitin Zaman Lafiya Na Jihar Kano Ya Yabawa Rundunar Yan Sanda Akan Kokarin Da Sukayi Na Kawo Zaman Lafiya A Dorayi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kwamitin Samar da zaman lafiya na jihar kano (KPC),yayi Allah wadai da abun da wasu batagarin matasa sukeyi a unguwar Dorayi na yin fadan daba da sauran wasu manyan laifuka.

Advertisement

Wannan na kunshe ne a cikin wani sagon murya da shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiya na jihar Amb. Ibrahim Waiyya ya rabawa manaima labarai ta hannun mataimaki na Musamman kan kafafen yada labarai, Bashir A Bashir.

Kasafin Kudi: Majalisar Dattawa Za Ta Duba Dakatarwar Da Aka Yi Wa Ningi – Akpabio

Kazalika Ambasada Ibrahim Waiyya ya bayyana cewa kwamitin zaman lafiya na Kano na yabawa rundunar yan sandan jihar kano Karkashin Jagorancin, CP Usaini Gumel duba da irin kokarin da sukayi na samar da tsaro cikin gaggauwa a yankin na Dorayi, tare da yadda aka samar da ofishin da zaiyi yakin da ayyukan daba a yankin da kewaye,harma da nasarar kama wasu daga cikin masu hannu da aikata wannan laifi.

Advertisement

Daga karshe Kwamitin zaman lafiya na jihar nan Kano Peace Committee yayi kira ga sauran alummar musamman na yankin Dorayi dasu cigaba da bawa Jami’an tsaro hadin kan da ya dace, musamman wajan bayar da bayanin sirri domin samun nasarar da ake bukata na yaki da fadan daba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending