News
Gwamnan Jihar Borno BabaganaZulum Ya Bukaci Sojojin Nijeriya Da Su Kafa Sansani A Dajin Sambisa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya bukaci sojojin Nijeriya da su kafa sansanin soji a dajin Sambisa, domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda yadda ya kamata.
Leadership ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne a wata ziyarar ban girma da mambobin kwamitin majalisar wakilai kan harkokin soji suka kai masa, ranar Laraba a Maiduguri.
Gwamnan ya kuma bukaci sojojin da su kafa sansanin soji a gabar tafkin Chadi da kuma tsaunin Mandara wanda har yanzu ya ci gaba da zama mafakar ‘yan ta’adda.
Ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da ta tabbatar da samar da isassun makamai don magance rashin tsaro.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
