News
Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Nada Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kaduna A Matsayin Uban Kungiya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar wakilan gidajen jaridu na ƙasa reshen jihar Kaduna (Correspondents Chapel) ta naɗa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Alhaji Sani Liman Kila a matsayin uban Ƙungiyar.
Da yake jawabi a wajen taron nadin da ya gudana a ofishin Shugaban ma’aikatan a fadar gwamnatin jihar Kaduna, shugaban kungiyar wakilan ‘Yan Jaridar Alhaji Abdulghaffar Alabelewa yace la’akari da irin kauna da gudummuwa da Sani Kila ke ba ‘yan jarida a faɗin jihar ne ya sa kungiyar ta karrama shi da mukamin uban Ƙungiyar.
Kotu Ta Yanke Wa Manajan Bankin FCMB Ɗaurin Shekaru 121 A Gidan Yari
Shugaban ‘yan jaridar ya ƙara da cewar ‘yan jarida a Jihar Kaduna a yanzu suna gudanar da ayyukan su cikin walwala da natsuwa saɓanin yadda abubuwa suke a baya inda ya bayyana hakan a matsayin kokari na shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin.
A jawabin sa shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin Alhaji Sani Liman Kila ya godewa Ƙungiyar ‘yan jaridar bisa ga wannan karramawa da suka yi mishi, inda ya bada tabbacin yin aiki kafada da kafada dasu.
“Yan jarida mutane masu muhimmanci a cikin al’umma waɗanda suna iya buɗewa da rufewa duk lokacin da suka ga dama, wannan karramawa da suka yi mini ta zama abin alfahari a gareni kasancewata mutum na farko da ya samu irin wannan matsayi, ina baku tabbacin kofofin mu za su kasance a buɗe gareku a kowane lokaci”.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
