Connect with us

News

Gwamnatin Tarraya ta damƙa tashar wutar lantarki ga sabon kamfani

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

An bayar da wannan umarni a ranar 30 ga Afrilu, wanda ke ƙunshe a cikin wata takarda wanda NERC ta fitar a ranar 30 ga Fabrairu, mai sa hannun Shugaban NERC, Sanusi Garba da Mataimakin sa, Musiliu Oseni.

Sun ce nan da kwanaki 30 TCN zai kammala tantance kadarori da basukan da za a gada domin sabon kamfanin shi ma ya gabatar da na sa kadarorin da basukan ga hukumar da kuma Hukumar Sayar da Hannayen Jari ta Ƙasa (BPE) kafin nan da ranar 30 Ga Yuni, 2024.

Advertisement

Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Nada Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kaduna A Matsayin Uban Kungiya

Daga kuma sai BPE ya kammala aikin danƙa tashar wutar lantarkin ga NISO ta hannun Hukumar Sayar da Kadarorin Gwamnati.

Premium Times ta ruwaito cewa wannan sabon tsari na NISO dai zai kasance dai shi ne ke da alhakin bayar da wuta musamman a yankunan da ake fama da wahalar wuta, wato waɗanda ke ƙarƙashin layin bayar da wuta na Osogbo.

Advertisement

Hakan ya na nufin NERC ya janye hannun sa ɗaya daga aikin bayar da lasisin wuta da ke hannun TCN, wanda ke raba ƙarfin wuta.

 

Advertisement

Kamar yadda Dokar Wutar Lantarki ta Ƙasa ta 2023, ta umarci NERC ta umarci BPE ya mayar da harkokin samar da wutar lantarki ga NISO.

 

Advertisement

Wannan ciniki dai ya ne daidai lokacin da ake fama da wahalar wutar lantarki a Najeriya.

 

Advertisement

Sannan kuma kwanan nan aka bayyana ƙarin kuɗin wutar lantarki mai ɗan karen tsada ga wasu sassan masu amfani da wutar lantarki.

 

Advertisement

Sai dai kuma kwanan baya Gwamnati ta ce za ta sake zuba kuɗin da ake tarawa daga janye tallafin wutar lantarki wajen inganta wutar lantarki, kiwon lafiya, da ilimi, inji Ministan Yaɗa Labarai

 

Advertisement

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sama da naira tiriliyan 1 da za a tara daga janye tallafin wutar lantarki za a sake zuba su ne wajen inganta wutar lantarki, kiwon lafiya, da ilimi ga ‘yan Nijeriya.

 

Advertisement

Da yake jawabi a matsayin babban baƙo na shahararren shirin Rediyo Nijeriya na Kaduna mai suna ‘Hannu Da Yawa’ a ranar Asabar a Kaduna, Idris ya ce a kusan kashi 40 na tallafin wutar lantarki, kashi 15 ne kawai masu amfani da wutar lantarki ke amfana wanda ya ƙunshi mawadata da gungun masana’antu, waɗanda ke jin daɗin wutar lantarki na kusan awanni 20.

 

Advertisement

Ya ce, “Yana da muhimmanci a jaddada cewa kuɗaɗen da za a ajiye daga janye tallafin wutar lantarki, za a sake zuba su ne wajen inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar nan da inganta sauran muhimman ayyukan jama’a kamar kiwon lafiya da ilimi. Kusan kashi 85 cikin ɗari na al’ummar da ke cikin sabon tsarin samar da wutar lantarki har yanzu suna samun tallafin.”

 

Advertisement

Ministan ya ce sabuwar dokar samar da wutar lantarki da Shugaban Ƙasa Tinubu ya sanya wa hannu ta ƙara ƙarfafa tsarin gudanar da ayyukan Hukumar Kula Da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) tare da bai wa hukumar damar sanya wa kamfanonin rarraba wutar lantarkin (DISCOs) tsauraran takunkumi kan laifukan da suka shafi kuɗi da samar da wutar ga masu amfani.

 

Advertisement

Idris ya kuma bayyana cewa kwamitin da Shugaban Ƙasa ya kafa domin duba tsarin tafiyar da Shirin Zuba Jarin Jama’a na Ƙasa ya gabatar da rahotonsa domin share fagen sake gudanar da shirye-shiryen, wanda zai bayar da tallafin kuɗi naira 25,000 ga talakawa miliyan 15 da magidanta masu rauni na tsawon watanni uku a tsakanin sauran ayyukan.

 

Advertisement

Ministan, wanda ya yi amfani da wannan dandali wajen kawar da maganar da wasu ke yi cewa wai gwamnatin Tinubu na shirin cutar da arewacin ƙasar nan, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da zuba kuɗaɗe wajen bunƙasa ayyuka a Arewa.

 

Advertisement

Ya yi nuni da cewa gwamnatin ta faɗaɗa noman alkama, shinkafa, rogo, da masara, a ƙarƙashin Shirin Noman Rani zuwa kadada 500,000 na gonaki.

 

Advertisement

Ya ce: “Shugaban Ƙasa ya umarce mu da mu fito mu ji halin da al’umma ke ciki, mu kawo masa rahoto. Mun je Dutse, Auyo, da Haɗeja, kuma mun tattauna da manoma game da nasarorin noman rani a waɗannan yankuna”.

 

Advertisement

Idris ya bayyana jin daɗin sa kan yadda a yanzu Jihar Kebbi ta zama cibiyar noman tumatur da sarrafa tumatur a ƙasar nan ta hanyar haɗin gwiwa da wani babban kamfanin sarrafa abinci mai suna GB Foods, wanda ya kafa wata masana’anta domin noman tumatur.

 

Advertisement

Ya ce manoma da dama, waɗanda galibin su mata ne, yanzu haka su na noman tumatur a Jihar Kebbi, saboda yanayin da ake samu da kuma tallafi daga GB Foods, wanda ya nuna matuƙar jajircewa wajen yin kasuwanci a Nijeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending