Connect with us

News

Sarkin Kuwait Sheikh Meshal Al-ahmad al-Sabah Ya Rusa Majalisar Dokokin Kasar

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rikicin siyasa da ya dabaibaye kafa gwamnati ya kai sarkin Kuwait Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah ga daukar matakin rusa majalisar dokokin kasar da nufin kawo karshen tarnaki wajen gudanarwar hukumomi.

Advertisement

Sakin Kowet Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah ya rusa majalisar dokokin kasar a ranar Juma’a tare da daukar nauyin wasu ayyukan gwamnati, makwannin shida kacal bayan zaben da aka gudanar a daular mai arzikin man fetur da ke yankin Gulf.

Inda Ranka: Yaron Da Ya Cire Ƙodarsa Ya Sayar Ya Sayi Wayar Hannu Ta N290,000’

Kamfanin dillanci labaran Kuwait na Kuna ya ruwaito cewa matakin wanda ya jibanci soke wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulki na tsawon shekaru hudu ya biyo bayan rikice-rikicen siyasa da suka kunno kai a kasar a baya-bayan nan.

Advertisement

Kamfanin na Kuna ya kuma kara da cewa sarki Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah da majalisar ministocin kasar za su ci gaba da tafiyar da ayyukan ‘yan majalisun domin kawo karshen tarnakin da wannan dambarwa ta siyasa ta kawo wajen gudanarwar hukumomi.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai sabuwar majalisar ta Kowet da aka zaba a farkon watan Afrilu ya kamata ta gudanar da zamanta na farko sa dai amma da dama daga cikin wakilan suka kaurarewa halartar wannan zama domin kin shiga gwamnati kamar yanda Dw ta ruwaito

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending