Connect with us

News

SERAP ta  Maka CBN A Kotu Kan Janye Wa Mutane Kuɗaɗensu A Asusunsu  Ajiyarsu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A wata gagarumar turjiya kan zabge wa mutane ‘yan kudadensu a asusun ajiyarsu da Babban bankin kasa, CBN ya ayyana da nufin tsaron yanar gizo na kudaden al’umma da ke asusun ajiyarsu, kungiyoyin kare hakkin dan Adam da sa ido kan harkokin hada-hadar kudaden al’umma (SERAP) da BudgIT da ‘136 concerned Nigerians’ sun maka CBN a Kotu.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa Kungiyoyin dai sun maka CBN a kotu ne saboda wani umarnin bankin na baya-bayan nan wanda ya umarci dukkan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi da su cire harajin tsaron yanar gizo ‘cybersecurity levy’ da kashi 0.5 cikin 100 akan duk wata hada-hadar kasuwanci ta yanar gizo.

Ba’Amurken nan na farko da a tarihi aka taɓa yi wa dashen ƙodar alade, ya mutu watanni biyu

Umurnin, wanda aka bayar a ranar 6 ga Mayu, 2024, masu shigar da kara sun yi wa karar ta su da lakabi “Umurni ba bisa doka ba”.

Advertisement

A cewar Kolawole Oluwadare, mataimakin daraktan SERAP, zabge wa mutane ‘yan kudadensu daga asusun ajiyarsu, ya zarce ikon babban bankin na CBN.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending