News
Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso za su kafa sabuwar kungiyar da suka kira AES
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kasashen uku dai duk sojoji ne ke mulkinsu a halin yanzu tun bayan da suka hambarar da gwamnatocin fararen hula.
Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da ke karkashin mulkin soja, sun kammala shirye-shiryen samar da kungiyar gamayyar kasashen, bayan da suka juya wa Faransa da ta yi musu mulkin mallaka baya, inda suka karkata akalarsu wajen Rasha a yanzu.
Ministocin harkokin wajen kasashen sun gudanar da wata ganawa a ranar Juma’a a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, domin cimma yarjejeniyar kafa kungiyar hadin kan kasashen Sahel wato AES.
Nijeriya Ce Koma Baya A Kasafin Kuɗin Ilimi A Yammacin Afirka –Kungiyar ASUU
A cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare ya fitar, ta ce shugabannin kasashen uku ne za su sanya hannu kan yarjejeniyar da suka cimma, duk da dai bai bayyana ranar da za a yi hakan ba.
A watan Janairun wannan shekarar ce kasashen uku suka sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS wacce suka zarga da zama ‘yar amshin shatan Faransa, don haka suka samar da ta su kungiyar.
Yankin Sahel dai na fama da matsalolin tsaro na kungiyoyin masu ikirarin jihadi, dalilin da ake ganin ya haifar da juyin Mulki a kasashen.
