Connect with us

News

Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Slow Rasuwa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Slow Rasuwa

Advertisement

Wannan na cikin wani sako da tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa, Mansura Isah ta wallafa a shafinta na Instagram da safiyar ranar Talata.

Mansura ta wallafa cewar “Innalillahi wainna illahi raji’un, Allah Ya yi wa Fati Slow rasuwa.

Advertisement

Saudi League: Ronaldo Ya Karya Tarihin Cin Kwallaye A Kakar Wasa Daya

“Allah Ya jikanta, Allah Ya yi mata rahama, ameen.”

Mansura ta ce tsohuwar jarumar ta rasu ne a wani gari Abasha da ke kusa da Sudan, kuma tuni aka yi jana’izarta a can.

Advertisement

A cewarta yanzu haka ana zaman makokinta a gidansu da ke Unguwa Uku a Jihar Kano.

Fati Slow a baya ta fice a harkar fim din Hausa kafin daga bisani ta yi batan-dabo.

Advertisement

Jarumar a shekarar da ta wuce ta sha tayar da kura a kafafen sada zumunta.

Leadership ta ruwaito cewa Tuni ‘yan masana’antar Kannywood da sauran al’ummar Musulmi suka shiga yi mata addu’ar samun rahama da Ubangiji.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending