Connect with us

News

Abba Kyari Zai Koma Gidan Kaso Na Kuje.

Published

on

Mataimakin kwamisshinan yan sanda wanda aka dakatar Abba Kyari

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wata babbar kotu da ke Abuja ta hana Mataimakin kwamisshinan yan sanda wanda aka dakatar Abba Kyari sabon beli. Saboda haka, zai koma gidan kaso na Kuje.

Advertisement

AIT ta ruwaito cewa Mai sharia Emeka Nwite lokacin da yake yanke hukuncin yace, bada belin wani abu ne da kotu in ta ga dama zata bayar ko akasin haka. Ya ƙara da cewa wanda ake ƙarar bai bada wani ƙwakwaran hujja da zai sanya kotu ta sake bada belin nashi.

Muna Duba Yiwuwar Saka Dokar Ta Baci A Kan Barkewar Annobar Kwalara – Hukumar NCDC

A 22 ga watan Mayu da ya wuce, kotun ta bada belin Abba Kyari domin bashi damar halartar janaizar mahaifiyar sa. Bayan wannan lokacin ya nemi alfarmar a ƙara masa sati ɗaya wanda kotun ta ƙara masa.

Advertisement

Sai dai a wannan karon, mai shari’a ya hana Abba kyari sabon belin, don haka dole yanzu ya koma gidan kaso na Kuje.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending