Connect with us

News

 Ya Kamanta Alkalai Su Rika Yin Tsatstsauran Hukunci Akan Dukkan Dan Daban Da Aka Kama Yana Cutar Da Alumma  —Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin jihar Kano ta ta bukaci Alkalai dasu rika yin tsatstsauran hukunci akan dukkan dan daban da aka kama da cutar da alumma .

Advertisement

Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin zaman majilisar zartarwa karo na 15 a fadar Gwamatin Jihar Kano.

EFCC ta kama Ma’aikatan banki biyu bisa zargin Satar  Sama Da Naira Miliyan 4 Na Wani Mamaci

Gwamnnan yace tuni shiri yayi nisa na kara bada tallafi jari ga matasa da iyaye mata Wanda zai tallafa wajen gudanar da sana”ar dogaro da kai.

Advertisement

Ya kuma kara da cewa acikin makwanni uku da suka gabata gwamnati ta Samar da fara aikin tituna sabbi da kuma gyara wadanda sukalalace a birni da karkara.

Ya kuma ce ganin shigowar damina gwamnati zata Samar da takin zamani ga manoma don rage musu radadi.

Advertisement

Gwamnan yace tuni gwamnati ta umarci kantomomin da suke rike da kananan hukumomi 44 dasu Samar da hanyoyi da kuma gyara magudanan ruwa don samun hanyoyin sufuri da gudun ambaliyyar ruwa a jihar.

Daga bisani ya ce gwamnati bazata zuba ido akan yanda wasu batagari suke shigo da bakin yan daba wadanda suka addabi kananan hukumomin Dala da Gwale da Karamar hukumar birni da sauran wurare daban daban a jihar inda yace tuni shiri yayi nisa wajen dakile su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending