Connect with us

News

EFCC ta kama Ma’aikatan banki biyu bisa zargin Satar  Sama Da Naira Miliyan 4 Na Wani Mamaci

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Tu’annati ta EFCC ta kama wasu tsoffin ma’aikatan bankin Union da ke Makurdi Babban Birnin Jihar Benue bisa zargin satar Naira 4,199,500 mallakin wani mai ajiya a bankin bayan da ya rasu.

Advertisement

Hakan na kunshe ne ta Cikin Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar EFCC, Dele Oyewale ya fitar ranar Asabar a Abuja, ya ce an kama wadanda ake zargin Idah Ogoh, da kuma Agbo Okwute ranar Juma’a a Makurdi.

Kimanin Yara 30,000 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Jihar Katsina Saboda Hare-Haren ‘Yan Bindiga

Oyewale ya ce kama su ya biyo bayan karar da bankin ya shigar a kansu kan zamba a asusun wani magidanci mai suna Emmanuel Azer Agenna.

Advertisement

A cewarsa, an bankaɗo badaƙalar tasu ne a lokacin da iyalan mamacin suka tunkari bankin domin neman ba’asin Asusun marigayin.

Ya ƙara da cewa, iyalan mamacin basu gamsu da ba’asin da bankin ya basu ba dangane da adadin da ke cikin asusun, inda daga bisani suka aika da koke ga bankin game da fitar wasu kuɗi ba tare da izini ba a asusun.

Advertisement

Ya ƙara da cewa, a bisa kokensu, bankin ya gudanar da bincike na cikin gida inda sakamakon binciken ya nuna cewa an cire kudi a asusun marigayin a ranar 10 ga watan Mayun 2023.

Daily Post ta ruwaito cewa Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending