News
Kimanin Yara 30,000 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Jihar Katsina Saboda Hare-Haren ‘Yan Bindiga
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kimanin yara 30,000 ne ba sa zuwa makaranta a jihar Katsina saboda ayyukan ‘yan bindiga.
Nigerian Tracker ta ruwaito cewa Babban mataimaki na musamman akan harka ‘yan bindiga da kuma ‘yan gudun hijira (lDP), Saidu lbrahim Danja ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Katsina.
Danja ya ce an samu wannan adadi ne bayan tantancewar da ofishinsa da kuma hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar a Binciken da suka gudanar.
A cewarsa, gwamnatin jihar Katsina ta fara mayar da yaran da abin ya shafa makaranta tare da basu kayan rubutu.
Danja ya ci gaba da bayanin cewa a halin yanzu jihar na da ‘yan gudun hijira 252,000 saboda ‘yan fashi da makami, inda ya kara da cewa: “Mun gaji ‘yan gudun hijira 278,000 a lokacin da muka karbi ragamar mulki daga gwamnatin baya.
Ya kara da cewa, “alkalumman ya ragu zuwa 252,000 yayin da sannu a hankali zaman lafiya ya dawo a yankunan da abin ya shafa.”
Danja ya ce saboda fargabar yiwuwar harin ‘yan bindigar, gwamnati ta rufe cibiyoyin lafiya kusan 52.
Ya kara da cewa gwamnati na hada kai da kungiyoyin kasa da kasa guda takwas domin inganta rayuwar wadanda rikicin ‘yan fashi ya shafa.
Haka zalika kungiyoyi masu zaman kansu suna taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a Katsina
