News
Da Dumi-Dumi :Shugaba Tinubu Ya Bai Wa Farfesa Attahiru Jega Mukami
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi sabon nadi ga tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega.
An bayyana nadin ne a lokacin da Tinubu ya kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan aiwatar da garambawul na kiwon dabbobi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Talata
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ya nada Jega a matsayin shugaban kwamitin da aka kafa domin magance matsalolin da ke kawo cikas ga aikin noma da buda sabbin damammaki da ke amfanar manoma, makiyaya, masu sarrafa kayayyaki, da masu rarrabawa a cikin tsarin kiwo
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa aiwatar da sauye-sauyen zai bukaci hadin kan mambobin kwamitin, wadanda suka fito daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu, da gwamnonin jihohi, yan Najeriya.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
