News
Bankwana ga mace ta musamman, jajirtacciya kuma gwarzuwa abar koyi: Florence Morenike Saraki
DAGA ABBA GWALE
Daman dai duk mai rai watarana dole zai ɗanɗani ɗacin mutuwa a duk lokacin da lokacinsa ya cika. Haka kuma rashin uwa mahaifiya ba ƙaramin rashi bane a wajen kowa.
Musamman ma idan aka ce Mahaifiyarka ta musamman ce, wadda tayi aiki tuƙuru a rayuwa da hidimtawa al’umma wajen sanya farin ciki a zuƙatansu.
Tabbas mutuwar Florence Morenike Saraki ba ƙaramin rashi aka yi ba, saboda ba iya kawai ƴaƴa da ƴan uwanta ba, gaba ɗaya mutanen gari da jihar Kwara dama Nigeria baki ɗaya sun yi rashi.
An haifi Florence Morenike Saraki a ranar 8 ga watan Agusta shekara ta 1935 a garin Owo dake jihar Ondo, kuma mace ce mai daraja da mutunci a cikin al’umma.
Marigayiya Florence Morenike Saraki ita kaɗai ce a wajen mahaifiyar ta, Felicia Ojomo da mahaifinta Mista Samuel Ibidapo Okunrinboye.
Mace ce mai tsayawa ta saurari mutane, tare da kula da iyalinta da ragowar ƴan uwa, mace ce wadda bata da son rai kuma abin hannunta baya tsone mata ido, tana da kyauta da karrama mutane.
Tayi karatu a Birtaniya, inda ta halarci kwalejin Balham & Tooting Bec a shekarar 1957 inda ta karanta fannin ilimin harkokin tsimi da tanadi, kafin kuma tayi digri a fannin shari’a, duka a Ingila.
Ta haɗu da mijinta, Olusola Saraki, a lokacin yana karantar harkar lafiya a shekarar 1961 a ƙasar ta Ingila.
Tabbas abin da Allah ya tsara sai ya faru, domin Olusola Saraki shi ne mijinta, wanda daga baya, bayan sun yi aure suka dawo Nigeria kuma ya zama shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ta ƙasa bayan ya tsunduma harkokin siyasa, bayan nan kuma ya zama Turakin Ilorin daga nan kuma ya samu ƙarin girma ya zama Wazirin Ilorin. A shekara ta 1962 ne kuma suka haifi Abubakar Bukola Saraki, ɗansu na farko, wanda shima sai da ya zama shugaban majalisar dattawa ta tarayyar Najeriya.
Ta gina rayuwar ta a kan ƙaunar juna da girmama mutane wanda shi ne jigo a nasarar da ta samu.
Ba ta da tsoro wajen bayyana ra’ayinta, sannan ba ta da ɓoye-ɓoye, ga zama da mutane da zuciya ɗaya, sai kyauta da jan mutane a jiki.
Tayi aiki da kamfanin Shell BP inda tayi aiki a sashen kula da Shari’a a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Ernest Shonekan wanda a lokacin shi ne shugaban sashen.
Bayan tayi ritaya daga kamfanin Shell BP kuma sai ta tsunduma harkokin Shari’a inda ta nuna ƙwarewarta a fannin.
Bugu da ƙari, ƴar kasuwa ce, wadda tayi sana’o’i kala-kala da suka haɗa da kasuwancin shinkafa da Tumatir da Sikari da ragowar kayan amfanin yau da kullum. Sannan tayi noma a jihar Kwara da garin Owo.
Ta samu kyaututtuka daban-daban bisa jajircewa da kuma taimakawa al’umma a rayuwa.
Ta rayu, rayuwa mai cike da walwala, ta mutu a ranar 18 ga watan Yuni na shekarar 2024. Tayi rayuwa wadda mutane da dama za su koyi darasi a ciki. Ta mutu ta bar ƴaƴa huɗu, ɗaya daga ciki shi ne Dr. Abubakar Bukola Saraki, sai ƙanwarsa, Sanata Gbemisola Saraki da ragowar guda biyun, Temitope da Laolu Saraki, waɗanda suma sun yi hidima ga al’umma.
Abubuwan da tayi na alheri suna da mutuƙar tasiri, kuma an gani a wajen ƴaƴanta, waɗanda suke bin abubuwan da tayi.
A ranar 19 ga watan Yuli na shekarar 2024 aka binne ta, ƴaƴa da jikoki da ƴaƴan jikoki sun yi bankwana da ita kuma za su ci gaba da yin Ayyuka na gari da take yi. Saboda ta bar musu abin da za su yi alfahari da shi.
Abba Gwale
Media Aid to Dr. Abubakar Bukola Saraki
