Connect with us

News

Karan farko jigo a jam, iyyar APC ya magantu Kan kuncin rayuwa da al, ummar Nigeria ke ciki

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma, Dakta Salihu Lukman, ya koka kan yadda Shugaba kasa Bola Tinubu ya jefa al’ummar ƙasar nan cikin wani yanayi na ƙunci sabida manufofinsa wanda hakan ke kara ta’azzara yanayin kuncin  rayuwar ga ƴan Nijeriya.

Lukman a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya yi mamakin irin yadda Tinubu ya ke nuna halin rashin ko in kula wajen gyara matsalolin ƙasar nan.

Advertisement

Ya ce ko ta fuskar gyara kalubalen da ƴan Najeriya ke fuskanta, Gwamnati ta nuna rashin sanin makama wajen gudanar da Gwamnati.

Tsohon jigon na APC ya ce sama da shekara daya magana ɗaya Shugaba Tinubu yake yi, tare da rashin kyakkyawar manufa da tsari wajen ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba.

Advertisement

Lukman ya ce “A kowace rana rashin tabbas na Gwamnati na ƙara fitowa fili.

Wannan yanayin da ya jefa al’ummar kasar cikin wani yanayi na rashin tabbas wanda ya ƙara haddasa tabarbarewar tattalin arzikin ƴan Nijeriya, shin wane shiri ne Shugaba Tinubu ya yi na gyara matsalar

Advertisement

daga karshe dai ya dasa ayar tambaya akan salon milkin Bola tinubu na rashin kyawawan manufa a sha,anin mulkin sa

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending