Connect with us

News

An Tsige Matashi Daga Sarautar Gargajiya Saboda Goyon Bayan Zanga-zanga 

Published

on

Abdullahi Isah sarautar gargajiya a matsayin Sarkin Matasan Bosso

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hakimin ƙaramar hukumar Bosso da ke jihar Neja, Muazu Adamu-Laka, ya tuɓe wa wani matashi mai fafutuka, Abdullahi Isah sarautar gargajiya a matsayin Sarkin Matasan Bosso saboda ya goyi bayan zanga-zangar yunwa da ƙuncin rayuwa da a ke shirin yi a faɗin kasar.

Advertisement

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa yankin yana cikin Masarautar Minna.

An tattaro cewa shugaban matasan ya fito fili ya goyi bayan zanga-zangar da aka shirya za a fara ranar 1 ga watan Agusta.

Advertisement

Ban Ji Ko ‘Dar’ Ba Game Da Goge Shafin Facebook Dina Ba —Rarara 

Sai dai a wata wasiƙar da a ka aike wa shi matashin, Isah mai ɗauke da kwanan watan 28 ga watan Yuli, sarkin ya buƙaci da ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban matasan Bosso.

“Na rubuto maka ne don sanar da kai cewa an kore ka daga muƙamin Shugaban Matasan Bosso daga ranar 28 ga Yuli, 2024.

Advertisement

“Ka da ka sake kiran kanka a matsayin Shugaban Matasan Bosso. Ina fatan za ka yi amfani da wannan bayanin da aka ba ka,” in ji wasiƙar.

Mista Laka ya ce al’umma ba za su amince da duk wani abu da zai lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending