Connect with us

News

Abubuwa Guda Shida Da Ke Jawo Rikidewar Zanga-Zangar Lumana Zuwa Tarzoma —Shehu Sani

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

 

Advertisement

Batun shirin fara zanga-zanga a Najeriya daga ranar 1 ga watan Agusta yana cigaba da tayar da kura da daukan hankalin masu mulki, hukumomin tsaro, malaman addini da na boko, da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin zamantakewa.

Gwamnati na tsoron cewa zanga-zangar, wacce aka bayyana cewa za ta kasance ta lumana, kan iya rikidewa zuwa tarzoma da tayar da hankali a Najeriya kamar yadda ya faru a baya, a shekarar 2020, lokacin zanga-zangar ‘ENDSARS’.

Advertisement

Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Gobir Tare Da Dan Sa.

A bangare daya, talakawan Nigeria sun ce zasu gudanar da zanga-zanga ne domin nuna fushinsu a kan halin matsi da kuncin rayuwa da kullum sai karuwa yake yi a yayin da masu rike da mukaman siyasa ke cigaba da fantamawa da dukiyar kasa.

Dan gwagwarmaya kuma tsohon Sanatan a jihar Kaduna Shehu Sani, ya yi nazarin wasu abubuwa guda shida da suke jawo zanga-zangar lumana ta rikide zuwa ta tarzoma.

Advertisement

Abu na farko da Shehu Sani ya ce yana kawo matsala lokacin zanga-zanga shine jami’an tsaro su yi amfani da alburushi na gaske wajen tarwatsa masu zanga-zanga.

Na biyu shine; batagari kan shiga cikin masu zanga-zanga domin su fasa shaguna, gidaje, da ofisoshi, da sauran dukiyar kasa da ta jama’a. Abu na uku shine; ana dauko hayar ‘yan daba domin su kaiwa masu zanga-zangar lumana farmaki.

Advertisement

Sai abu na hudu; rashin sauraron tsawatarwar shugabanni ko jagororin zanga-zanga. Na biyar kuma shine; batun barkewar rigima a tsakanin kungiyoyin dake zanga-zanga.

Sai abu na shida wanda shine shigar wasu mutane masu boyayyiyar muguwar manufa cikin masu zanga-zang

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending