Connect with us

News

Yadda Farashin Man Fetur Ya Kai N1,300 A Wasu Jihohi A Faɗin Nijeriya.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Sakamakon bushewa da rijiyoyin man fetur da dama su ka yi, an samu layuka a gidajen mai a jihohin Kano, Legas, Kaduna, Ribas, wasu yankuna na Abuja, Nija da wasu jihohi a faɗin Nijeriya.

Advertisement

NIGERIAN TRACKER ta ruwaito cewa, hakan ya sa ƴan bunburutu su ke amfani da damarsu wajen sayar da duk lita ɗaya a farashin N1,300 da N1,500 a jihohin Legas da Ogun.

Tsadar Rayuwa: Masu Zanga-zanga Sun Datse Hanyar Shiga Abuja Yayin Da Sojoji Sun Kafa Shinge Kan Titin Abuja 

An fara samun yawaitar layin man ne tun ranar Asabar a jihohin inda kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce hakan na faruwa ne sakamakon tseko da ake samu wajen ɗakko man daga rijiyoyin saboda matsalolin ƙafewa da ake fuskanta,

Advertisement

Duk da tabbatacin shawo kan matsalolin da NNPC ya bayar, lamarin ƙara ƙamari ya ke musamman a manyan biranen ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, babu motoci da aka zuba wa mai a rijiyoyin Legas a ranar Lahadi.

Advertisement

Wani ma’aikaci da ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya ce babu mai a kusan dukkan rijiyoyin man a ranar Lahadi wanda hakan ya sa aka samu jinkiri daga gare su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending